Home >>
BAMBANCE-BAMBACEN DA KE TSAKANIN MAGANAR FATAR BAKI DA RUBUTATTAR MAGANA: KEBABBEN NAZARI A HARSHEN HAUSA
Khadija Isma’il

ABSTRACT
Manufar wannan makala ta ce gano bambance-bambancen da ke tsakanin maganar fatar baki da rubutattar Magana a harshen Hausa. A cikin wannan takarda za a nuna irin ka’idojin da aka tanada a cikin rubutu don su taimaki mai karatu gane harafi tare da sauran abubuwa wadanda ba ayyanawa musamman ta fuskar ma’ana da yadda za a fade su. Ana ganin cewa idan mutum ya san wadannan ka’idojin to ba zai sha wuyar karatu ba, kuma ba za a sami kura-kurai a cikin abin da ya rubuta ba, ko ya fada saboda wata basirar harshe da yake da ita, wadda aka kira competence ko intuition knowledge.


Full Text