Home >>
SHI'A A SAKKWATO DAGA SHIGOWARTA ZUWA RUGUJEWARTA MAQALA CE
Idris Garba

ABSTRACT
Da sunan Allah Mai rahama Mai jinqai. Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya yi umurni da bin sunna, ya kuma tsoratar daga bin bidi'a. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammadu (S.A.W), da Iyalan gidansa, da Sahabbansa, da wadanda suka bi su da kyautatawa har tashin Alqiyama. Bayan haka, shi'anci wata mummunar aqida ce da ta yadu a duniyar musulmi har ta zama musu wata annoba, ta kunno kai a cikin Nijeriya ta kafa tutarta a Zariya ta kuma bude rassanta a duk jihohin Nijeriya. Jihar Sakkwato na daya daga cikin jihohin da ake samun mabiya shi'anci, ya kuma yadu zuwa qananan hukumominta. Kasancewar Sakkwato cibiyar Daular Usmaniyya wurin da Shehu Usmanu ya jaddada Addinin Musulunci a qarni na goma sha tara (19), mabiya aqidar shi'a sun ci karo da jayayya da tankiya daga al'ummar Sakkwato har ya yi sanadiyyar tarwatsewar 'yan shi'ar.


Full Text