Home >>
SUNAYEN LAQABI A AL 'ADAR HAUSAWAShamsuddeen Isma?ila da Muhammad Abubakar ZabiABSTRACT
Hausawa al’umma ce mai riqo da al’ada, wato Hausawa sun rayu a lokacin gargajiya bisa matakan
rayuwa har guda uku. Ya fara tun daga haifuwa da aure da kuma mutuwa. A wannan mataki Hausawa
sun yi amfani da sunaye iri-iri na gargajiya. Hatta bautarsu a gargajiya suka gudanar da ita a wancan
lokaci. Haka kuma sun gudanar da rayuwa bayan karbar addinin Musulunci duk da haka ba su watsar
da al’adunsu na gargajiya ba, wajen sanya wa ýaýansu laqabi irin nasu na gargajiya. Kuma
sakamakon haduwarsu da Larabawa sun samu tasirin haduwa da su tafuskar Sunaye wanda ya qara
samarwa Hausawa sunayen laqabi. A cikin wannan takarda za a dubi sunayen Hausawa lokacin
gargajiya tare da sunayen lokaci da sanadi da yanayi da sunayen siffa. Sannan za a duba sunayen
Hausawa bayan zuwan musulunci da sunayen asali da sunayen laqabi a al’dar Hausawa. A qarshe,
kammalawa za ta biyo baya kafin manazartar takardar da za ta biyo baya.
Full Text